Gwamnatin jihar Kebbi ta ayyana Juma'a 22, Satumba ranar hutu


Gwamnatin Jihar Kebbi karkashin Jagoracin Gwamnan Jihar Sen Abubakar Atiku Bagudu ta ware gobe Juma'a  1 Al-Muharram 1439 AH Wanda ya yi daidai da 22/09/2017 a Matsayin Hutu, na Sabuwar Shekarar Musulunci.

Wannan ya biyo Bayan sanarwar da Mai Alfarma Sarkin Musulim, Sa'adu Abubakar lll ya fitar na ganin jinjirin Watan Al-Muharram 1439 yau a fadarsa da ke Sokoto.

Kuma Maigirma Gwamnan Jihar Kebbi Sen Abubakar Atiku Bagudu ya tara Sarakun Gargajiya yau a Fadar Gwamnatin Jihar, da su bada Wannan sanarwar a Masallatan Juma'a tare da yi ma kasa addu'ar zama lafiya da kuma Kara ma shugaban kasa Muhammad Buhari Kwarin guiwa wajen gudanar da Mulkin sa.


Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Gwamnatin jihar Kebbi ta ayyana Juma'a 22, Satumba ranar hutu Gwamnatin jihar Kebbi ta ayyana Juma'a 22, Satumba ranar hutu Reviewed by on September 22, 2017 Rating: 5

No comments:

Rubuta ra ayin ka

ISYAKU TV

Powered by Blogger.