Fiye da mutum 1000 sun rasa matsuguni a Kebbi sakamakon ambaliyar ruwa

A makon da ya gabata rafin kwara ya cika ya batse yanayi da ya haifar da ambaliyar ruwa a kauyuka 15 da ke Dole-kaina da Bagudo a jihar Kebbi.

Fiye da gidaje 700,dabbobi,amfanin gona da aka yi kusan girbewa da sauran kayakin rayuwa suna daga cikin ababen da suka salwanta a ambaliyar.

Bayanai daga hukumar bayar da agaji na gaggawa na jihar Kebbi (SEMA) ya nuna cewa gidaje 115, Mata 115 da yara 567 ne lamarin ya rutsa da su a Dole-kaina yayin da ake fargaban cewa fiye da mutum 1000 sun rasa matsuguni.


Kauyukan da ambaliyar ruwan ya mamaye sun hada da Shiyar Magaji, Shiyar Kokari, Sabon Gari, Manahare, Tungar Noma da Dole-Kaina duka a karamar hukumar Dandi.Sai kuma Tungar Mai Goda, Bakin Wuya, Malami, Kanshiba, Tungar Tutu, Tungar Giris da Tungar Lalea a Bagudo.

Gwamnatin jihar Kebbi ta tura wata tawaga dauke da kayan taimakon gaggawa zuwa yankin tare da kwararru domin agaza wa wadanda lamarin ya rutsa da su. 


Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN