Fitattun barayin motoci sun fada hannun jami'an tsaro

Wasu shahararrun barayin motoci guda 4 sun fada hannun jami'an tsaro a jihar Benue.Wadanda aka kama sun hada da dan shekara 27 Monday Otupa, Joseph Oriyan, 27, Basil Fabian 39 da Mike Onazi, 34.

Mutanen da aka kama sun yi bayani cewa sukan yi amfani da karuwai domin tattara bayanai kafin su aiwatar da fashi ko kwacen mota daga bayin Allah.

Sun kuma kara da cewa suna da mambobin kungiyarsu a jihohi da dama wadanda suke tuntuba kafin su aiwatar da hari.

Kowane mutum yana da nasa aiki kamar rewaya,mai fenti,bakanike da sauransu.

Ga masu shawara,aiko labari ko korafi ku rubuto zuwa isyakulabari@gmail.com Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Fitattun barayin motoci sun fada hannun jami'an tsaro Fitattun barayin motoci sun fada hannun jami'an tsaro Reviewed by on September 30, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.