El-Rufai ya gana da shugaba Buhari,ya caccaki Mama Taraba

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-rufai ya caccaki ministan harkokin mata Aisha Alhassan wadda ake kira Mama Taraba sakamakon kalamai da tayi wadda ya nuna yadda ta fito kiri kiri tana goyon bayan Atiku Abubbakar akan ya fito ya zama dan takaran shugaban kasa a 2019.

El-rufai ya shaida wa manema labaran fadar shugaban kasa hakan jim kadan bayan ganawarsa da shugaba Buhari.

Gwamna El-rufai ya ce bai yi mamakin ganin Aisha Alhassan ta bijirewa Shugaba Buhari ba domin tun asali bata tare da tawagar manufar Buhari tun 2015 kuma bata zabi Buhari ba lokacin zaben fitar da dantakara na jam'iyar APC kuma bata taba goyon bayan manufar Shugaba Muhammadu Buhari ba.

Daga bisani El-rufai ya kara da cewa Shugaba Buhari yayi biris da shawarar da manyan jigogi a jam'iyar APC suka bashi tun farko akan Aisha Alhassan ,saboda haka ci gaba ko jingine Aisha a yanzu ya ta'allaka ne a tunanin Shugaba Buhari.

Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN