• Labaran yau

  September 10, 2017

  DSS ta kama wadanda suka shirya kai hari lokacin Sallar Layya a wasu jihohi

  Hukumar ayyukan tsaro da leken asiri na cikin gida DSS ta yi nassarar cafke wasu masu tsastsaurar ra'ayin Islama da suka shirya kai hare hare a lokacin bukukuwan Sallar Layya da ya gabata.

  Sanarwar hakan ya fito daga hannun mai magana da yawun hukumar Mr Tony Opuiyo wadda ya ce 'yan ta'addan sun shirya kai hare-haren ne a Abuja, Kano, Kaduna, Niger, Bauchi, Yobe da Borno.

  Opuiyo yace wadanda aka kama sun shirya akan zasu yi amfani da bama-bamai da kisan kan mai uwa da wabi ta hanyar yin amfani da bindigogi masu sarrafa kansu domin su buda wuta a wajajen cinkoso na jama'a lokacin shagul gular Sallah.

  Rundunar ta ce ta yi nassarar damke wani  Moses Peverga a Abuja wadda shi ne ke samar da makamai ga bata gari a jihar Benue lamarin da ya sa ake samun aikata mugan laifuka ta hanyar yin amfani da makaman.

  Haka zalika rundunar ta cafke Abdulkadir Mohamm, Muhammad Ali, da Husseini Mai-Tangaran a birnin Kano bisa zargin su da kitsa shirin hari da akayi niyyar kaiwa lokacin bukukuwan Sallar Layya a birnin Kano da kewaye.

  Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: DSS ta kama wadanda suka shirya kai hari lokacin Sallar Layya a wasu jihohi Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama