Dillalan makamai sun fada hannun jami'an tsaro

Sojojin runduna ta 1 tare da hadin guiwar jami'an tsaron DSS sun kama wasu mutum 2 da ake zargi da dillancin makamai ba bisa ka'ida ba.An kama Abdulkarim Jibrin da Suleiman akan hanyar Funtua zuwa Gusau dauke da albarusai 1.479 da 7.62mm na musamman a wata mota Gulf mai lamba AWE-534-AA (Nasarawa).

Binciken farko ya nuna cewa mutanen zasu kai wa batagari makaman ne kafin a cafke su.

Wata majiya ta labarta cewa mutanen suna fuskantar bincike a hannun jami'an tsaron DSS.


Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Dillalan makamai sun fada hannun jami'an tsaro Dillalan makamai sun fada hannun jami'an tsaro Reviewed by on September 27, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Ku dakace mu
Powered by Blogger.