Dan Luwadi ya kashe Saurayi domin yana soyayya da Yarinya

Labarai da ke fitowa daga birnin Abuja sun nuna cewa wani sanannen dan Luwadi mai suna Samarola Musa ya kashe wani yaro da ke koyon aiki a shagonsa wadda kuma ya batashi ta hanyar tilasta shi yin luwadi da shi a garin Lugbe na babban birnin tarayya Abuja.

Lamarin ya faru ne bayan shi Musa dan Luwadi ya kama yaron nasa mai suna Ademola Adeshina yana zina da wata yarinya lamarin da ya harzuka Musa ya rufe Ademola da duka daga bisani kuma ya mutu.

Punch Metro ta ruwaito cewa Musa ya shaida wa mahaifin yaron cewa Ademola ya mutu ne sakamakon cutar Malaria, amma yarinyar da ta shaida abin da ya faru ta musanta wa Mahaifin Ademola. Sakamakon haka  Mahaifin ya shaida wa 'yan sanda kuma ya bukaci a gudanar da bincike akan gawar.

Daga bisani sakamakon bincken ya nuna cewa Musa yana yi wa Ademola Luwadi kuma an tabbatar da raunuka a cikin jikinsa da zasu iya zama musabbabin mutuwarsa.

Kotu ta adana wadda ake zargin a gidan Yari har zuwa ranar Litinin 20 ga watan Nuwamba 2017.Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Dan Luwadi ya kashe Saurayi domin yana soyayya da Yarinya Dan Luwadi ya kashe Saurayi domin yana soyayya da Yarinya Reviewed by on September 20, 2017 Rating: 5

No comments:

Rubuta ra ayin ka

ISYAKU TV

Powered by Blogger.