• Labaran yau

  September 08, 2017

  Da dumi dumi ! 'Yan sanda a Jos sun sake kama wanda ya kashe yarinya ya tsere a hannun CID

  Rahotanni da ke fitowa yanzu yanzu sun nuna cewa hukumar 'yan sanda ta sake kama saurayin nan da ya kashe wata yarinya 'yar shekara 8 kuma ya cire wasu sassan jikinta a Port Harcourt 'yan makonnin baya Ifeanyi Dike da daren jiya a Jos na jihar Plateu.

  Bayanai sun nuna cewa yanzu haka ana ta murna a hedikwatan rundunar 'yan sanda na jihar Rivers yayinda rundunar ta jihar Plateu ta shaida wa rundunar ta jihar  Rivers cewa ta kama Ifeanyi Dike.

  Tserewar Ifeanyi daga hannun sashen CID na rundunar 'yan sandar ta jihar Rivers ya yi sanadin korar wani Sajen na 'yan sanda tare da tsare wani safeton 'yan sanda a jihar ta Rivers.  Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Da dumi dumi ! 'Yan sanda a Jos sun sake kama wanda ya kashe yarinya ya tsere a hannun CID Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama