• Labaran yau

  September 06, 2017

  Bullar cutar amai da gudawa ya kashe mutum 20 a jihar Kebbi

  Mutum 20 sun mutu sakamakon bullar cutar amai da gudawa a jihar Kebbi a lamari da ya fi kamari a kananan hukumomin  Shanga, Birnin Kebbi, Fakai da Koko/Besse.

  Haka zalika cutar ta shafi mazauna  Tungar Buzu, Korama,  Samanaji da Keri a karamar hukumar Shanga lamarinda tuni ya haifar da fargaba a garin Tungar Buzu da kewaye kamar yadda wani mazunin Tungar Buzu Abdullahi Usman ya shaida wa Daily Trust.

  Bayanai sun nuna cewa Gwamnatin jihar Kebbi tana sane da lamarin kuma tuni ta tura magunguna,kayan agaji da kwararru zuwa yankin da lamarin ya shafa domin a shawo kan cutar daga ci gaba da yaduwa.

   


  Shafin mu na Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Bullar cutar amai da gudawa ya kashe mutum 20 a jihar Kebbi Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama