B-kebbi: Aikin ruwa na Dukku yaci Naira Milyan 900

Kwangilar fadada aikin ruwa na Dukku a garin Birnin kebbi zai ci zunzurutun kudi har Naira Miliyan 900.Bayanin haka ya fito ne daga bakin shugaban tsari da ka'ida  Alhaji Muhammed Sirajo Garba wadda ya kara da cewa shirin zai samar da wadataccen ruwan sha a garin Birnin kebbi da kewaye kuma ana kyautata zaton za'a kammala aikin a cikin shekara daya da rabi.

Garba ya ci gaba da cewa zuwan karin bututun ruwa da aka gani an kawo a manyan motoci 15 daga kasar China ya tabbatar cewa gaba dayan kayakin zasu zo ne daga Kamfanin kai tsaye daga kasar China.

Gwamnatin jihar Kebbi ta baiwa Kamfanin Zhorghan na kasar China kwangilar aikin fadada gidan ruwa na Dukku wadda shine gidan ruwa da yake ba garin Birnin kebbi ruwa.

Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN