An sace mataimakin kwamishinan 'yan sanda

Rahotanni a jihar Kaduna na nuna cewa an sace wani mataimakin kwamishinan 'yan sanda tare da matarsa a yayin da suke tafiya a mota. An sace mataimakin kwamishinan nan ne a wani dajin da ke tsakanin Funtua a jihar Katsina da kuma Birnin Gwari a jihar Kaduna.

BBC ta ruwaito cewa dajin da aka sace wannan mataimakin kwamishinan 'yan sanda dai dama sanannen wuri ne da aka yi amannar na kunshe da 'yan ta'adda kamar 'yan fashi da barayin shanu da masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa.

Har yanzu dai rundunar 'yan sanda ta jihar ba ta ce komai ba kan wannan batu.


Ga masu shawara,aiko labari ko korafi ku rubuto zuwa isyakulabari@gmail.com Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
An sace mataimakin kwamishinan 'yan sanda An sace mataimakin kwamishinan 'yan sanda Reviewed by on September 28, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.