An kama 'dan sandan bogi da mukamin Sgt

Rundunar 'yan sanda a jihar Rivers ta kama wani dansandan bogi Sgt.Benjamin Tanko sanye da tufafin 'yansanda a garejin mota na Oil Mill a garin Port Harcourt ranar Laraba.

Sashen sa ido na musamman na safeto janar na 'yan sanda a jihar River karkashin jagorancin SP Grace Wanwo ta kama Benjamin. An sami katin shaida na 'yansanda har kala uku a gurinsa wadda ke dauke da lambar aikin 'dansanda da suka banbanta da juna.

Benjamin dan asalin garin Kajuru a karamar hukumar Kajuru na jihar Kaduna zai bayyana gaban kuliya idan an kammala bincike kamar yadda majiyarmu ta labarta.
Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
An kama 'dan sandan bogi da mukamin Sgt An kama 'dan sandan bogi da mukamin Sgt Reviewed by Isyaku Garba on September 16, 2017 Rating: 5

No comments:

Rubuta ra ayin ka

Powered by Blogger.