Amarya ta jefa 'diyan uwargida su 2 a cikin rijiya sakamakon kishi

Wata mata mai suna Aisha kuma Amarya ga wani Alhaji Isah mazauni garin  Yelwan-Bassa a karamar hukumar Kokona na jihar Nassarawa ta jefa 'yayan kishiyarta cikin rijiya sakamakon kishi.

Yaran guda biyu Zainab yar shekara 4 da Baba dan shekara 2 'ya'yan uwargidan ce.

Kakakin hukumar 'yansanda na jihar DSP Kennedy Idrisu ya ce binciken da 'yan sanda suka gudanar ya nuna cewa tsananin kishi ne kawai yasa Aisha ta jefa yaran a cikin rijiya,haka zalika binciken ya gano cewa Aisha masifaffar mace ce da ke gana wa uwargidan ukuba ta hanyar aikata ababe da ka iya janyo fitina a gidan.
 
Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Amarya ta jefa 'diyan uwargida su 2 a cikin rijiya sakamakon kishi Amarya ta jefa 'diyan uwargida su 2 a cikin rijiya sakamakon kishi Reviewed by on September 19, 2017 Rating: 5

No comments:

Rubuta ra ayin ka

ISYAKU TV

Powered by Blogger.