• Labaran yau

  August 17, 2017

  "Zan warkar da Buhari idan yazo wajena don addu'a" - Satguru Maharaj

  Shugaban tafiyar addinin One Love Family Satguru  Maharaj yace zai warkar da shugaba Muhammadu Buhari matukar yazo wajensa don samun addu'a,Maharaj yayi wannan furucin ne yayinda yake zantawa da manema labarai a sakatariyar 'yan jarida da ke Alausa a Ikeja na jihar Lagos jiya 16 ga watan Agusta.

  Maharaj ya kara da cewa shugaban Najeriya babban mutum ne kuma haka ya kamata ya kasance,"shi yasa idan Buhari yazo wajena zan taimake shi kamar yadda na taimaki tsohon shugaban Najeriya Ibrahim Badamasi Babangida akan matsalar ciwon kafa amma sai ya gujeni daga baya shi yasa ciwon ya sake dawowa".

  Ya kuma kara da cewa Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya cancanci a jinjina mashi sakamakon yadda yake tafiyar da lamurran kasannan a bisa tsari duk da yake shugaba Buhari bayanan.


   
  Shafin mu na Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120. Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120. Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu.
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: "Zan warkar da Buhari idan yazo wajena don addu'a" - Satguru Maharaj Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama