'Yar shekara 24 ta ci zaben majalisar wakilai a Kenya

Cynthia Jepkosgei Muge 'yar shekara 24 wadda ta kammala karatunta na Digiri a fannin tsare-tsare birni na zamani ta lashe zaben kujerar takaran majalisar wakilai na  MCA a  mazabar Kilibwoni ,gundumar Nandi na kasar Kenya.

Yarinyar wadda ta kasa samun kudade da zata sayi fom na 'yan takara a karkashin wata jam'iya ta yanke shawaran tsayawa ita kadai tilau ba karkashin wata jam'iya ba kuma sakamakon hakan ta lashe zabe inda ta doke abokin hamayyarta da kuri'u  8760 yayin da abokin hamayyarta Wilson Kiptanui ya sami kuri'u 8354.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120. Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120. Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.
'Yar shekara 24 ta ci zaben majalisar wakilai a Kenya 'Yar shekara 24 ta ci zaben majalisar wakilai a Kenya Reviewed by on August 12, 2017 Rating: 5

No comments:

Rubuta ra ayin ka

ISYAKU TV

Powered by Blogger.