'Yan Najeriya da suka dawo daga Libya sun sami agajin N25.000

Isyaku Garba - Birnin kebbi

Kimanin yan Najeriya 262 ne mazauna kasar Libya suka dawo gida Najeriya karkashin kulawar kungiyar hukumar da ke taimaka wa harkokin shige da fice na duniya (International Organisation for Migration IOM).

Hukumar bayar da taimakon gaggawa ta kasa NEMA ce ta dauki dawainiyar isowar 'yan Najeriyan a babban sansanin Alhazai na jihar Lagos a filin saukan jiragen sama na Murtala Muhammed a Ikeja.

Bayanai sun nuna Cewa IOM ta baiwa kowane mutum N18.000 yayin da NEMA ta basu N7000 domin a taimaka masu da abinda zasu koma garuruwansu.

Hukumomin tsaro da suka shaida lamarin sun hada da Hukumar 'yan sanda,DSS, NAPTIP ,FAAN da rundunar sojan sama ta Najeriya.


Ku biyo mu a
https://www.facebook.com/isyakuweb
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120.
Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120.
Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN