• Labaran yau

  August 01, 2017

  Birnin kebbi - Yadda tarbon Osinbajo ya shafi 'yan makaranta

   Isyaku Garba - Birnin kebbi

  A bisa tsarin shirin tarbon mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo a ziyararsa zuwa jihar Kebbi,jera yara 'yan makaranta na cikin shirin wanda hakan yasa aka jera dalibai 'yan makaranta a kan wasu manyan tituna a cikin garin Birnin kebbi tun karfe 8:30 na safe har zuwa yanzu suna nan a jere akan wadannan tituna.

  Wani yaro mai suna Ahmadu wadda yace shi dalibi ne a makarantar sakandare na Nagari da ke cikin Birnin kebbi ya tabbata mana cewa shi dai rana ce ta dame shi kuma yana fama da kishin ruwa.

  Haka lamarin yake a wasu hanyoyi da ake kyautata zaton mataimakin shugaban kasa zai bi.

  A ci gaba da zagayawa da muka yi a cikin garin Birnin kebbi wadda ke dauke da jami'an tsaro a gurare masu mahimmanci ,jama'a na ci gaba da gudanar da ayyukansu kamar yadda suka saba a kullum face kasancewar dalibai da jami'an tsaron a titunan Birnin kebbi da zai lurar da mutum cewa za'a sami babban bako a Birnin kebbi.   
  Ku biyo mu a
  https://www.facebook.com/isyakuweb
  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120.
  Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120.
  Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Birnin kebbi - Yadda tarbon Osinbajo ya shafi 'yan makaranta Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama