Shugaba Buhari ya koma kan aiki

Shugaba Muhammadu Buhari ya koma bakin aiki,hakan ya biyo bayan wata takarda da ya rubuta wa majalisar daddijai da ta wakilai inda yake sanar da su cewa zai koma bakin aikinsa a ranar Litinin 21 ga watan Agusta 2017.

Bayanin haka ya fito daga bakin mai magana da yawun shugaban kasa Femi Adesina wadda yace shugaban yayi haka a bisa tanadin kundin tsarin mulki na Najeriya.

A cikin wasikar, shugaban ya rubuta cewa, "Kamar yadda sashe na 145 na kundin tsarin mulkin 1999 ya tanada, Na rubuta wannan wasika ce domin na sanar da ku cewa na koma bakin aikina a matsayin shugaban Najeriya, daga ranar Litinin, 21 ga watan Agusta, 2017, bayan na dawo daga ganin likitocina a Birtaniya."
A ranar 7 ga watan Mayun 2017 ne, Shugaban Buhari ya mika ragamar gwamnati ga mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo, wanda ya zama mukaddashin shugaban kasa, a lokacin da ba ya nan.


Shafin mu na Facebook
https://www.facebook.com/isyakuweb
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120.
Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120.
Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu.
Shugaba Buhari ya koma kan aiki Shugaba Buhari ya koma kan aiki Reviewed by on August 21, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.