Osinbajo na nan da karfin ikonsa da kundin tsarin mulki ya ba shi - Buhari

Mai magana da yawun shugaban Najeriya Garba Shehu ya musanta labari da wata jarida ta wallafa 'yan kwanakin baya inda take zargin cewa an ware Maitaimakin shugaban kasa daga harkokin sha'anin mulki tun lokacin da shugaba Muhammadu Buhari ya dawo daga doguwar jinya da yayi a London.

Garba Shehu ya kara da cewa Mataimakin shugaban kasa Prof.Yemi Osinbajo yana nan da martaba da kuma darajar sa kuma ana damawa da shi kamar yadda kundin tsarin mulki na Najeriya ya tanada.

"Wannan magana karya ce da jita-jita, maganganu ne marasa tushe da ake kirkiro don ganin an shiga tsakanin wadannan shugabanni masu kwazo," in ji sanarwar.

"Wannan maganar ba abar kamawa ba ce, a ce daga dawowar shugaban kasar cikin mako guda har an fara batun ware mataimakinsa cikin harkokin mulki.

"Abin da nake so a sani shi ne, shi Mr Osinbajo shi ne mutum na kut-da-kut ga shugaban kuma mashawarcinsa na musamman."

Malam Garba Shehu ya kara da cewa, cikin mako guda da ya gabata bayan dawowar Shugaba Buhari, Farfesa Osinbajo ya halarci tarurruka daban-daban a madadin shugaban, 'in ban da sallar Juma'a.'


Shafin mu na Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120. Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120. Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN