• Labaran yau

  August 23, 2017

  "Ni fa ban ce zan sha guba in mutu ba idan Buhari ya dawo" - Ayo Fayose

  Gwamnan jihar Ekiti Ayo Fayose ya musanta cewa yace zai sha guba domin ya mutu idan har shugaba Buhari ya dawo Najeriya lafiya kalau da ranshi kamar yadda jita-jita ke zagayawa a shafukan sada zumunta na yanar gizo musamman a ranar 22 ga watan July.

  A wata hira da yayi da jaridar Premium Times mai magana da yawun Gwamna Fayose Idowu Adelusi ya kara haske akan cewa "babu inda Gwamna fayose yayi wannan zance masoma aikin 'ya'yan jam'iyar APC ne da suke kirkire-kirkiren  batutuwan karya domin su karkatar da hankalin jama'a akan gaskiyar rashin lafiyar shugaba Buhari".
  Shafin mu na Facebook
  https://www.facebook.com/isyakuweb
  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120.
  Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120.
  Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu.
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: "Ni fa ban ce zan sha guba in mutu ba idan Buhari ya dawo" - Ayo Fayose Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama