Mutum 3 sun mutu a fada tsakanin manoma da makiyaya a Benue

Kimanin mutum uku ne suka mutu a wani tashin hankali da ya gudana tsakanin manoma da makiyaya a garin  Akpagodogbo na karamar hukumar Otukpo a jihar Benue.

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne bayan zargin cewa shanayen makiyaya Fulani sun bi ta kan gonakin manoma inda suka haifar da barna a gonaakin.

Takaddama ta taso bayan manoman sun fuskanci makiyayan akan lamarin da ya  rikide ya zama fada da ya haifar da karin barna kan wasu gonakin da kuma mutuwar shanaye da mutum uku.

Tuni dai aka tura jami'an 'yan sanda da suka shawo kan lamarin.


Ku biyo mu a https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120. Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120. Shiga www.isyaku.com don samun cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.
Mutum 3 sun mutu a fada tsakanin manoma da makiyaya a Benue Mutum 3 sun mutu a fada tsakanin manoma da makiyaya a Benue Reviewed by on August 10, 2017 Rating: 5

No comments:

Rubuta ra ayin ka

ISYAKU TV

Powered by Blogger.