Matasa sun yi wa junansu munanan raunuka

Tashin hankali tsakanin al'umman Ojobo a cikin jihar Delta yayi sanadin samun munanan raunukka tsakanin Matasa da suka yi wa junansu raunuka da adda ta hanyar sara a safiyar ranar Juma'a 4/8/2017.

Bayanai sun nuna cewa rikicin ya  samo asaline bayan an kammala zabe na shugabancin al'umman Ojodo 'yan watanni da suka gabata wanda a lokacin wasu matasa suka so su kawo cikas akan lamarin zaben amma aka shawo kansu.

Daga bisani sunyi ta yin barazana ga zaman lafiyan jama'a bayan mutumin da suke so ya sha kashi a hannun takwaransa a lokacin zaben shugabancin al'umman.

Lamarinda ya janyo a ranar Juma'a sauran Matasan gari suka nemi kare jama'a daga barazanar matasan na farko lamarinda ya kai ga raunata matasan sassan guda biyu.

Tuni dai jami'an tsaro suka shawo kan lamarin kuma komai ya koma daidai a garin Ojobo.


Ku biyo mu a
https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120.
Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120.
Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.
Matasa sun yi wa junansu munanan raunuka Matasa sun yi wa junansu munanan raunuka Reviewed by on August 05, 2017 Rating: 5

No comments:

Rubuta ra ayin ka

ISYAKU TV

Powered by Blogger.