Kasuwar Saminaka a yau

Yau laraba itace ranarda kasuwar Saminaka ke ci.Kwatsam ba zato ba tsammani sai ruwan sama ya sauka kamar da bakin kwarya.

Wannan ruwan dai bai yiwa 'yan kasuwa dadi ba  a zagayen da nayi , musamman layin Turakun Awaki inda na sami Awaki sharkab sunsha ruwa sosai.

Haka zalika na zagayi layin Hatsi (ma'auna) can ma naga abin baiyi Musu dadi ba.
 
Na tambayi wani dillalin Awaki cewa ya kake ganin Awaki yau a wannan kasuwa ?

Yace mini "gaskiya ba haka suka so ba ! Amma dole suyi hakuri da hukuncin Allah. Yanuna mini cewa da yawa wasu awakai sai sunsami  matsala sanadiyar wannan ruwan da suka Sha".

Daga Sani Musa Saminaka


Shafin mu na Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120. Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120. Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu.
Kasuwar Saminaka a yau Kasuwar Saminaka a yau Reviewed by on August 30, 2017 Rating: 5

No comments:

Rubuta ra ayin ka

ISYAKU TV

Powered by Blogger.