Karamar yarinya ta gane mai satan yara a Sokoto

Wata karamar yarinya a rukunin gidaje 5000 da ke birnin Sokoto ta tona asirin wani matashi da yataba yunkurin sace ta bayan ta shaida shi a ranar Assabar data gabata.

Lamarin da yasa wasu matasa a unguwar suka bincike shi inda shi da kansa ya shaida masu cewa ya saci yara da dama kafin ita karamar yarinyar ta gane shi.

Wanda ake zargin dai yaki ya fada ko su waye yake sayarwa yaran idan ya sato su.

Bayanai sun nuna cewa an mika matashin ga hukumar 'yan sanda domin su ci gaba da bincike.


Ku biyo mu a https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120. Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120. Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.
Karamar yarinya ta gane mai satan yara a Sokoto Karamar yarinya ta gane mai satan yara a Sokoto Reviewed by on August 09, 2017 Rating: 5

No comments:

Rubuta ra ayin ka

ISYAKU TV

Powered by Blogger.