Kakakin Majalisar dokoki a jihar Kogi yayi murabus

 Isyaku Garba - Birnin kebbi

Kakakin majalisar dokoki na jihar  Kogi  Umar Ahmed Iman yayi murabus kwana daya bayan majalisar ta dage zamanta sakamakon takaddamar da ta taso a cikin majalisar.

Magatakardar majalisar ne ya karanta wa 'yan majalisar takardar murabus da kakakin ya yi abinda ya kaiga kada kuri'ar da ya kai ga zaben Homourable Kolawole a matsayin sabon kakakin majalisar dokokin wanda dan gaban goshin Gwamna Yahaya Bello ne na jihar ta Kogi.

Bayanai sun nuna cewa takaddamar ta taso ne ranar Talata bisa cece-kuce a kan zancen cire shugaban masu rinjaye na majalisar wanda hakan ya rikide zuwa mataki da majalisar ta sami kanta a yanzu.
Ku biyo mu a
https://www.facebook.com/isyakuweb
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120.
Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120.
Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.
Kakakin Majalisar dokoki a jihar Kogi yayi murabus Kakakin Majalisar dokoki a jihar Kogi yayi murabus Reviewed by on August 03, 2017 Rating: 5

No comments:

Rubuta ra ayin ka

ISYAKU TV

Powered by Blogger.