Igbo na Najeriya basa da asali da Yahudawan Isra'ila - Sakamakon DNA

Tunani da fatan shugaban kungiyar al'umman Igbo wadanda ke alakanta asalin kabilar Igbo da kasancewa Yahudawa na kasar Isra'ila  (Re­deemed Israel Commu­nity of Nazarene Association RICON) ya gamu da cikas wanda ya biyo bayan sakamakon wani gwaji da aka fitar wadda ya nuna cewa ba abinda ya alakanta kabilar Igbo na Najeriya da Yahudun kasar Isra'ila.

Shugaban kungiyar muryar Yahudawa na Duniya (The international President of Jewish Voice Ministries) Rab­bi Jonathan Bernis shine ya bayar da sanarwar haka  a Uruagu-Nnewia yayin da yake gabatar da sakamakon gwajin da aka yi a dakin gwaje gwaje na kwayoyin halitta na DNA (Deoxyribonucleic acid) a garin Houston na kasar Amurka.

An karbi miyau daga Igbo 124 daga al'umma daban daban a Nnewi na jihar Anambara saboda a gudanar da gwajin na Y25,DNA a ranar 6 da 7 na Fabrairun 2017.Ku biyo mu a
https://www.facebook.com/isyakuweb
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120.
Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120.
Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.
Igbo na Najeriya basa da asali da Yahudawan Isra'ila - Sakamakon DNA Igbo na Najeriya basa da asali da Yahudawan Isra'ila - Sakamakon DNA Reviewed by on August 07, 2017 Rating: 5

No comments:

Rubuta ra ayin ka

ISYAKU TV

Powered by Blogger.