Hotuna - Yadda aka kusan kone mai satan mutane

Yadda satan mutane ya zama ruwan dare a kudanci da wasu sassa na Arewacin Najeriya haka daukan doka a hannu ya zama ruwan dare wajen kona mutane da ake zargi da aikata laifuka kamar satan mutane,ko kasancewa dan kungiyar asiri ko fashi da makami ko su sha dukan tsiya har sai rai ya fita.

Wadannan hotuna wani mutum ne da ake zargi da cewa mai satan mutane ne da ya gamu da fushin wasu mutane a unguwar Ikeja a garin Lagos wadanda suka yi yunkurin kona shi da ransa bayan sun zuba mashi fetur kamar yadda ka gani a hoto.

Wanda ake zargin ya auna sa'a sakamakon zuwan jami'an tsaro a wajen kuma suka kamashi suka tafi da shi ofishinsu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120. Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120. Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.
Hotuna - Yadda aka kusan kone mai satan mutane Hotuna - Yadda aka kusan kone mai satan mutane Reviewed by on August 12, 2017 Rating: 5

No comments:

Rubuta ra ayin ka

ISYAKU TV

Powered by Blogger.