• Labaran yau

  August 27, 2017

  Hotuna - Rigimar Fulani da Igbo da ya kai ga sara da adda

  Rahotanni da ke fitowa daga jihar Enugu sun nuna cewa an sami kwarya kwaryar tashin hankali tsakanin Fulani da wasu matasa 'yan kabilar Igbo a Ozalla na karamar hukumar Nkanu ta kudu inda ake zargin cewa wani Fulani ya sassare wani mutum Ndubueze Oboro a gonarsa a dajin Umane Ngene ta kudu.

  Bayanai sun nuna cewa Bafullacen ya sare Ndubueze a kafada da yatsunsa a cikin gonarsa lamarin da ya sa matasa a kauyen suka yi gangami suka je farutar Bafullacen.

  Garin neman Bafullacen ne matasan suka tarar da wani Bafullace daban mai suna Abdulrahman Abdullahi inda suka afka masa da duka da sara shi ma suka jikata shi kafin jami'an tsaro su kawo masa dauki ,lamarin da ya sa jami'an tsaron suka kai Igbo da Fulani da lamarin ya rutsa da su Asibiti.
  Shafin mu na Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120. Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120. Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu.
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Hotuna - Rigimar Fulani da Igbo da ya kai ga sara da adda Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama