• Labaran yau

  August 30, 2017

  Hotuna - Mai satan mutane Evans ya amsa laifinsa a Kotu

  Shahararren mai satan mutane wadda ya azurta da biliyoyin naira sakamakon wannan aikin  Chukwudumeme Onwuamadike wadda aka  fi sani da suna Evans ya gurfana yau a gaban Kotu a garin Lagos.

  Evans da wasu mutum biyar sun gurfana a gaban Kotu kuma Evans ya amsa laifinda aka tuhumeshi da aikatawa na hadin baki a aikata laifi da satan mutane domin ayi garkuwa da su.

  Alkalin Kotun ya dage shara'ar zuwa ranar 19 ga watan October yayin da ya yi ummarni a ci gaba da tsare wadanda ake tuhumar a gidan Yari na Kiri kiri.

  Shafin mu na Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120. Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120. Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu.
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Hotuna - Mai satan mutane Evans ya amsa laifinsa a Kotu Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama