Hotuna- Mahaifi yayi wa 'yarsa mai shekara 2 fyade

Wata mai fafutukar kare 'yancin bil'adama a garin Kaduna tana bukatar ayi wa wata 'yar karamar yarinya 'yar shekara biyu mai suna Maimunatu Shehu wadda ake zargin cewa mahaifinta ya yi mata fyade kana ya azabtar da ita.

Bayanai sun nuna cewa yanzu haka yarinyar wadda take cikin halin tausayi tana karbar magani a Asibiti jihar Kaduna.

Mai fafutukar kare 'yancin bil'adamar ta roki Gwamnatin jihar Kaduna akan cewa ta taimaka domin ayi wa Maimunatu adalci saboda zargin cewa akwai rade-radin cewa 'yanuwan mahaifinta suna kai kawo domin su sa mahaifin ya kaucewa fuskantar hukunci akan cewa wai yana da tabin hankali.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120. Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120. Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.
Hotuna- Mahaifi yayi wa 'yarsa mai shekara 2 fyade Hotuna- Mahaifi yayi wa 'yarsa mai shekara 2 fyade Reviewed by on August 12, 2017 Rating: 5

No comments:

Rubuta ra ayin ka

ISYAKU TV

Powered by Blogger.