• Labaran yau

  August 26, 2017

  Hotuna - Ko ka san Taj Mahal ba Masallaci bane Hotel ne ?

  Tun shekarun baya da hotunan Taj Mahal ya fara bayyana a kasar Hausa kimanin shekaru 25 da suka gabata,mutane da dama a Arewacin Najeriya kan yi amfani da hotunan Taj Mahal tamkar hoton wani kayataccen Masallaci.

  Amma gaskiyar lamarin shine Taj Mahal ba Masallaci bane asali ma Taj Mahal Hotel ne.

  Taj Mahal an ginashi ne a birnin Mumbai na kasar India wadda kamfanin Tata ta kaddamar da ginin a 1903 kuma mashahuran masu zane zanen gini Sitaram Khanderao Vaidya da D. N. Mirza suka zana taswirar ginin Taj Mahal a 1973 daga bisani Melton Bekker.ya tsara hasumiyar ginin a 2008 wadda yasa ginin ya yi kama da Masallaci.

  Duk da yake Hotel na Taj Mahal ya fuskanci harkar ta'addanci inda wasu 'yan ta'adda suka yi garkuwa da mutane da dama bayan sun halaka wasu a 2010 a ckin Taj Mahal hakan bai hana ginin samun ci gaba da ingancin martabarta ba sakamakon ci gaba da samun tagomashi wajen karbar manyan mutane a Duniya kamar shugaba Bill Clinton da Barak Obama na kasar Amurka.
  Shafin mu na Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120. Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120. Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu.
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Hotuna - Ko ka san Taj Mahal ba Masallaci bane Hotel ne ? Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama