Hotuna - Tserewar wanda ya kashe yarinya ya gudu a hannun yansanda ya janyo zanga zanga

Idan kuna biye da mu,kwanaki mun ruwaito maku labarin yadda wani dalibi na jami'ar kimiyya na Port Harcourt ya yi wa wata yariya 'yar shekara 8 fyade daga bisani ya kasheta kuma ya kwakwale idanunta daga karshe ya yi gunduwa gunduwa da jikinta lamarinda ya kaishi ga fadawa hannun 'yansanda a garin na Port Harcourt.
KARANTA Ya kashe 'yar shekara 7 ya jefar da gawa a bola
Kwana biyu da kasancewa hannun 'yansanda sai aka samu labarin cewa  Ifeanyi Dike ya tsere daga hannun 'yansandan lamarinda yasa wasu matasa suka fara zanga zangar neman adalci da bayani daga hukumomi ta yadda wadda ake tuhumar zai tsere daga hannun hukuma bayan ya aikata irin wannan mumunar laifin.
KARANTA Kalli yadda wannan matashi ya cire ido,harshe da nonon wannan yarinya
Masu zanga zangar sun kona tayoyi a kan hanyoyi musamman a unguwar EliOzu a jihar ta Rivers.

Kalli hotuna a kasa:
Shafin mu na Facebook
https://www.facebook.com/isyakuweb
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120.
Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120.
Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu.
Hotuna - Tserewar wanda ya kashe yarinya ya gudu a hannun yansanda ya janyo zanga zanga Hotuna - Tserewar wanda ya kashe yarinya ya gudu a hannun yansanda ya janyo zanga zanga Reviewed by on August 23, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.