• Labaran yau

  August 24, 2017

  Hotuna - Dan shekara 27 ya auri baturiya yar shekara 72

  Angela wata tsohuwace yar kasar Ingila mai shekara 72 wadda ta sadu da CJ a shafin sada zumunta na Facebook watanni uku da suka gabata,lamarin da ya haifar da soyayya tsakanin su wadda kuma hakan ya kai ga ziyara da Angela ta kawo wa CJ a Najeriya kuma daga bisani aka daura masu aure duk da yake wannan ne karon farko da suka hadu ido da ido a rayuwarsu kuma aka daura auren.

  Angela wadda tsohuwra 'yar taxi ce a Dorchester tace ta kashe fiye da Pound 20,000 domin ta ziyarci masoyinta a Najeriya kuma ta gamsu da yadda ta ganshi ido da ido.

  Amma tace ta gamu da mamaki yadda hukumomi a Ingila suka kasa samar wa sabon mijin nata Visa zuwa kasar Ingila har sau uku.

  Ta kara da cewa duk da kalubale da ta fuskanta wajen shigar da sabon mijin nata kasar Ingila wadda mil 4000 ne daga Najeriya tace har yanzu zukatansu na tare a dankon soyayya.


  Angela dai yar shekara 72 tana da jikoki uku yayinda CJ dan shekara 27 wannan ne karo na farko da yayi aure a rayuwarsa.

  Kalli hotuna a kasa:  Shafin mu na Facebook
  https://www.facebook.com/isyakuweb
  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120.
  Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120.
  Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu.
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Hotuna - Dan shekara 27 ya auri baturiya yar shekara 72 Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama