Dutse mai girman km 4.4 zai bi kusa da Duniyar mu ranar 1 ga Satumba

Wani katon dutse da yake ci da wuta a cikin al'arshin Allah zai biyo ta kusa da Duniyarmu ta Earth ranar 1 ga watan Satumba a tazara ta kimanin miliyan 7 tsakaninsa da Duniyarmu kamar yadda cibiyar binciken sararin samaniya na Amurka NASA ta ambato.

Dunkulallen dutsen da akayi wa suna Astroid Florence ya samo sunansa ne daga Florence Nighangale (1820-1910) wadda shine ya kirkiro tsarin aikin jinya Nurse na zamani.

Dutsen Astroid Florence ya kai girman kilomita 4.4 kamar yadda na'urar hangen sararin samaniya na Spitzer ya gano wadda ke girke a dakin NEOWISE na harkokin sararin samaniyya mallakar NASA.

Astroid Florence shi ne dunkulallen dutse mafi girma da zai wuce mafi kusa da Duniyarmu ta Earth tun lokacin da aka fara binciken gano duwatsu da ke wucewa ta kusa da Duniyar tamu inji Mr.Jodas shugaban dakin binciken.

Bincike ya nuna cewa tun daga 1890 ba a sami dutsen da ya wuce mafi kusa da Duniyarmu ta Earth ba sai a yanzu 2017 kuma baza'a sake samun irin wannan ba sai a 2500.


Isyaku Garba - Birnin kebbi


Shafin mu na Facebook
https://www.facebook.com/isyakuweb
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120.
Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120.
Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu.
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN