• Labaran yau

  August 30, 2017

  Buhari ya ba 'yan kungiyar D’Tigress N1m kowanensu sakamakon nassarar zama zakarun Africa

  Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi bakoncin ziyarar kungiyar kwallon kwando na Najeriya D’Tigress yau a fadar shugaban kasa a Abuja.

  D’Tigress tayi nassarar lashe gasar kwallon kwando na Africa a karon farko cikin shekara 12  da suka gabata a wasar karshe da aka buga ranar Lahadi da ya gabata a kasar Mali.

  Bayanai sun nuna cewa Gwamnati  ta saka wa kowace 'yar wasa da Naira miliyan daya yayinda masu jagorantarsu zasu sami rabin miliyan kowanensu.

  Kalli hotunan ziyarar a kasa:  Shafin mu na Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120. Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120. Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu.
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Buhari ya ba 'yan kungiyar D’Tigress N1m kowanensu sakamakon nassarar zama zakarun Africa Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama