Boko haram ta yanka manoma 42 'yan garin Aliero

ISYAKU.COM ya samu sanarwa cewa labari na kasa kuskure ne aka samu wajen fahimtar kalaman mai Girma Gwamnan jihar Kebbi Alh.Atiku Bagudu  yayin da yake bayarda misali wa jami'an Majalisar dinkin Duniya akan lamarin da ya faru da wasu manoma 'yan asalin garin Aliero shekarar bara a Borno ba wai sabon lamari bane.ISYAKU.COM ya gode da fahimta irin naku

Karanta Labarin kamar yadda Kwamishinan watsa Labarai na jihar Kebbi ya shaida mana

Kimanin mutum 42 ake zargin boko haram ta yanka su a jihar Borno 'yan asalin karamar hukumar mulki ta Aliero da ke jihar kebbi yayin da suka je jihar Borno domin suyi aikin noma.Gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi ya shaida haka yayin da yake karbar bakoncin wakilan kungiyar lafiya ta majalisar dinkin duniya a ranar Laraba.

Daily Post ta ruwaito cewa Gwamna Atiku ya shaida wa wakilan na majalisan dinkin duniya cewa wani Kwamishinansa ya kira shi inda ya shaida masa cewa an kashe wasu manoma 42 da suka je noma a Borno amma an bar mutum 1 da rai domin ya koma gida ya shaida wa jama'a lamarin da ya faru da sauran a Borno kuma ana zargin cewa kungiyar boko haram ce ta kashe su ta hanyar yankan rago.

Bayanai sun nuna cewa kimanin 'yan gudun hijira 7000 yan Najeriya dasuka ketara zuwa jamhuriyar Niger aka dawo da su jihar Kebbi wadda hakan ya kara haifar da matsala da tuni ake fama da ita wajen harakar rigakafin yara kanana.

Isyaku Garba - Birnin kebbi




Shafin mu na Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120. Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120. Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu.
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN