• Labaran yau

  August 16, 2017

  Bayan ya yi wa diyarsa fyade ya tilasta ta zubar da ciki sau 3

  Rundunar 'yansanda a jihar Kano ta kama wani Nuruddeen Abubakar dan shekara 40 bisa zargin yi wa diyarsa 'yar shekara 14 fyade da ya kaita ga samun ciki da ya tilasta ta zubar da shi.

  Kakakin hukumar yan sanda na jihar Kano  DSP Magaji Musa Majia ya shaida haka yayin da yake gabatar da wasu da ake tuhuma da aikata laifuka daban daban ga manema labarai ranar Talata 15,Agusta.

  DSP Magaji ya kara da cewa lamarin fyade a jihar Kano ya zama wani laifi da ake yawan aikata shi saboda daga 1 ga watan Agusta zuwa 15 ga watan Agusta rundunar ta kama mutum 34.

  Haka zalika ya ci gaba da bayani cewa Nuruddeen Abubakar dan shekara 40 mazauni rukunin gidajen unguwa uku yayi wa diyar cikinsa 'yar shekara 14 fyade,sai  Musbahu Ibrahim dan shekara 25 mazauni rukunin gidaje na Zangon Marikita ya shiga hannu saboda yi wa diyar Kawunsa fyade.

  Wani Pasto Samuel John na lamba 26 Whether-head unguwar Sabon gari shima ya shiga hannu saboda zargin yiwa wasu yara biyu tagwaye 'yan shekara 13 wadda diyan wani Pasto ne abokin aikinshi tare da wata 'yar shekara 11 fyade.
  Su kuma Dahiru Haruna da Hamza Lawan daga rukunin gidaje na  Sheka an kamasu ne bisa zargin hada baki inda suka aikata ba daidai ba ga wani yaro dan shekara 9.


  Shafin mu na Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120. Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120. Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu.
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Bayan ya yi wa diyarsa fyade ya tilasta ta zubar da ciki sau 3 Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama