• Labaran yau

  August 29, 2017

  Barawon rogo ya shake mai gonan rogo har lahira

  Wani matashi dan shekara 33 mai suna Azeez Kilani ya fada hannun hukumar 'yan sanda na jihar Ogun bayan an zarge shi da kashe wani mutum mai suna David Adima a gonarsa na rogo a kauyen Sojuju ta hanyar shakeshi har lahira a cikin gonar .

  Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne ranar 13/8/2017 bayan mai gonar David ya kama barawon rogo Azeez a cikin gonarsa yayin da yake kan satar rogo ta hanyar tugewa lamarin da ya janyo kita-kita da ya kai ga kokuwa da yasa Azeez ya shake David har lahira saboda kada ya tona masa asiri.

  Azeez yana daya daga cikin mutum 42 da Kwamishinan yan sanda na jihar Ogun Ahmed Iliyasu ya gabatar da su yayin zantawa da yan jarida a hedikwatar rundunar a Abeokuta.


  Shafin mu na Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120. Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120. Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu.y
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Barawon rogo ya shake mai gonan rogo har lahira Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama