• Labaran yau

  August 23, 2017

  "Ba zamu lamunci Malaman bogi da masu shaye-shaye ba" - Gwamna Atiku Bagudu

  Gwamna Atiku Bagudu ya bukaci kungiyar malamai ta kasa NUJ akan ta dauki mataki domin ta shawo kan yawan karuwan Malamai wadanda ke ma'amala da kayan maye da shaye-shaye a fadin jihar Kebbi.

  Gwamna Atiku ya furta haka ne yayin da yake karbar bakoncin shugabannin kungiyar ta NUJ a gidan Gwamnati a garin Birnin kebbi wadanda suka kai masa ziyara.Atiku yace babu yadda jihar Kebbi zata samu cin gaba matukar tana fama da kashi 30% na Malaman bogi ko masu shaye-shaye.

  A nashi jawabi shugaban kungiyar malamai ta kasa comrade Mike Aloba Olukoya yace yazo jihar Kebbi ne domin ya halarci taron kungiyar ta Malamai na kasa da ake gudanarwa a garin Birnin kebbi na jijar Kebbi


  Shafin mu na Facebook
  https://www.facebook.com/isyakuweb
  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120.
  Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120.
  Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu.
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: "Ba zamu lamunci Malaman bogi da masu shaye-shaye ba" - Gwamna Atiku Bagudu Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama