B-kebbi - Labarin matar da ta mayar da rabin jikin mijinta maciji zuki-ta-malle ne

Kimanin makonni biyu da suka gabata aka sami wata jita-jita  mai  karfin gaske da yayi ta zagayawa a ciki da wajen garin Birnin kebbi wadda ya samo asali daga karamar hukumar Bunza da ke cikin jihar Kebbi inda ake ta yayata cewa wata mata tayi wa kishiyarta asiri amma sai tasirin asirin ya kama mijinta lamarinda yasa rabin jikinsa ya zama na maciji rabi kuma na dan adam.

Bisa bukatar masoya shafinmu ISYAKU.COM ya binciko ko yaya gaskiyar lamarin yake saboda a gaya wa jama'ar garin Birnin kebbi da kuma jihar Kebbi gaskiyar abun da ya faru.

Da farko dai ISYAKU.COM ya tuntubi kakakin hukumar yan sanda na jihar Kebbi  ko akwai masaniya game da wannan lamarin inda bayanai suka nuna cewa babu kamshin gaskiya game  da wannan zancen a bangaren hukumar yan sanda domin babu kara da aka shigar ko koke da ya shafi irin wannan lamari.

ISYAKU.COM ya bincika a Kotun gangaren Takalau wajenda ake jita-jita cewa anan ne ake shara'ar wannan lamari.Majiyarmu ta shaida mana cewa babu kamshin gaskiya game da lamarin.haka zalika Majiyar tamu ta shida mana cewa kimanin makonni biyu da suka wuce kwatsam sai suka  gan jama'a suna dafifi a gaban Kotun ,lokacin da suka bincika ko miye ke faruwa sai aka ce wai "ana shara'ar wata mata da ta mayar da mijinta maciji" a wannan Kotu shine dalilin da ya sa jama'a suka zo domin su gan abun al'ajabi .

Majiyar tamu ta kara da cewa yayinda jama'a ke dafifi a gaban Kotun Alkali da ma'aikatan Kotun suna cikin Kotun kuma basu san ko miye ke faruwa ba face lokacinda suka lura taron jama'a ya wuce yadda hankali zai iya lissaftawa,ganin cewa babu wata shara'a da ke gaban wannan Kotun da ya jibanci irin wannan matsalar sai mahukunta suka rufe Kotun domin kada jama'a su dauki doka a hannunsu akan abinda ba zahiri bane.

Rufe Kotun ke da wuya bayanai sun nuna cewa wasu daga cikin jama'a suka balle makulli da aka rufe Kotun da shi wai ala tilas an rufe lamarin a cikin Kotu ne,majiyar tamu ta ci gaba da yi mana bayani cewa bayan jama'a sun balle makullin Kotu suka shiga suka ga lallai babu wani abu a zahiri da zai tabbatar da wanna lamarin amma wasu jama'a suka ki barin harabar Kotun har Magariba.

ISYAKU.COM ya bukaci wanda ya ga lamarin da idonsa kuma ya mallaki hoton lamarin ya kawo ofishinsa za'a bashi tukwuicin N2000 amma har yanzu babu wanda ya zo kuma babu wanda ya tabbatar da lamarin.wanda haka ya tabbatar cewa wannan zancen ba komi bane face zuki-ta-malle daga mutane da suka shahara wajen kirkire-kirkiren jita-jita saboda rashin aiki.

Isyaku Garba daga Birnin kebbi


Shafin mu na Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120. Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120. Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN