An kashe wani mutum bisa zargin satan yara

Wani mutum da ba'a shaida ko waye ba ya gamu da ajalinsa bayan ya sha dukan tsiya a hannun wasu matasa a unguwar Brown Street a Akinpelu, Oshodi na garin Lagos bayan an kama shi da jakar ghana must go dauke da yara uku ranar Talata

Bayanai sun nuna cewa mazauna unguwar sun gan wadda ake zargin daike da jakar ta gana must go kuma yana ta fama da jakar dalilin da ya sa aka bincike shi lamarin da yasa aka gano yara uku a cikin jakar biyu a mace daya da ransa.

Wani bayani ya yi karin haske akan cewa wadda aka kashe da farko yace shi malamin wata makarantar Firamare ne a Odeogberin International Nursery and Primary School a Owoseni Street a cikin Oshodi
amma bayan da aka tuntubi shugaban Makarantar da Headmaster sai suka ce su kam basu sanshi ba lamarinda ya kara harzuka matasa da yasa suka kashe shi da duka.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sanda na jihar Lagos ASP Olarinde Famous-Cole ya tabbatar da faruwar lamarin da ya kira "hukuncin jahiliyya" domin bayanin da suka samu daga DPO na Akinpelu ya nuna cewa an kashe mutumin ne a bisa zargin satan yara amma babu wani ko wata da yazo caji ofis yayi kara akan cewa anyi yunkurin satan dansa ko an sace yaronsa kawo yanzu.

Tuni dai rundunar 'yansandan ta kame wasu mutane da tace suna taimaka mata ne akan binciken da take yi akan lamarin
Shafin mu na Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120. Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120. Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu.
An kashe wani mutum bisa zargin satan yara An kashe wani mutum bisa zargin satan yara Reviewed by on August 16, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.