An kammala jigilar Alhazan jihar Kebbi yayin da jirgi na 9 ya sauka Saudiya

An kammala jigilar Maniyyata na jihar Kebbi yayin da jirgi na tara kuma na karshe ya sauka lafiya kalau yau a kasar Saudi Arabia.

Jigilar da kamfanin sufurin jirgin sama na Max Air ya kammala bai ci karo da manyan matsaloli ba yayin aikin jigilar Maniyyatan a aikin jigilar Maniyyata na bana wadda jirage tara ne suka tashi a gaba dayan aikin jigilar a jihar Kebbi.

Jirgi na tara kuma na karshe yana dauke da Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Samaila Dabai Yombe,Amirul Hajj na bana wadda shine Mai Martaba Sarkin Zuru Dr Sani Sami,Uwar gidan Gwamnan jihar Kebbi Haj.Aisha Atiku Bagudu da sauran manyan jami'an Gwamnati da manyan 'yan siyasar jihar Kebbi .




Shafin mu na Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120. Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120. Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN