An daure matar da ta kone duwawun yarinya shekara 1 a Kurkuku

Alkalin wani Kotun Majistare a garin Kaduna ya daure wata mata mai suna  Kemi Stephen tsawon shekara daya bisa samunta da laifin gallazawa diyar maigidanta mai suna Hilda Joseph ta hanyar kona duwawun yariyar 'yar shekara 10 da wuta.

Bayanai sun nuna cewa yarinyar tana zaune da Kawunta a unguwar Goningora a jihar Kaduna,amma sai matar Kawunta Kemi tayi ta gallaza mata ta hanyar duka,hanata abinci daga bisani sai ta kona duwawun yarinyar da wuta bisa zargin yarinyar ta aikata ba daidai ba.

Hukuncin wadda aka yanke a Kotu ta 7 a Barnawa Kaduna zai tabbatar da cewa Kemi wadda ke dauke da tsohon juna biyu ta yi zaman gidan Kurkuku tsawon shekara daya sabanin shekara biyar da aka yanke mata da farko wadda aka rage zuwa shekara daya albarkacin tsohon juna biyu da take dauke da shi.


Ku biyo mu a
https://www.facebook.com/isyakuweb
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120.
Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120.
Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.
An daure matar da ta kone duwawun yarinya shekara 1 a Kurkuku An daure matar da ta kone duwawun yarinya shekara 1 a Kurkuku Reviewed by on August 06, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.