• Labaran yau

  July 17, 2017

  'Yar kunar bakin wake ta kashe mutum 10 a Masallaci

  Rahotanni daga birnin Maiduguri sun nuna cewa da safiyar yau Litinin wata 'yar kunar bakin wake ta kashe mutum goma a wani Masallaci lokacin sallar asuba yayin da ta tayar da bom da ke daure a jikinta.

  Fashewar bom din ya haifar da mutuwar ita kanta da mutum gomma yayinda wadanda suka jikata aka garzaya dasu Asibiti.

  'Yan kungiyar boko haram da suka dade suna kai irin wadannan hareharen tun bayan lokacin da sojojin Najeriya suka addabesu a dajin Sambisa basu fito suka dauki alhakin kai harin na yau ba.  Ku biyo mu a shafin mu na Facebook @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka sami labaranmu ta Whatsapp ? ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye kyauta a koda yaushe muka wallafa Labari. Kana da sha'awar taimaka mana da Labarai, ko sharhi ? ka kira mu a 08062543120. Shiga shafinmu kai tsaye domin samun cikakkun Labarai.Ka shiga www.isyaku.com a browser ko opera ko firefox ko safari na wayarka zaka sami cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: 'Yar kunar bakin wake ta kashe mutum 10 a Masallaci Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama