Yadda wadatar lantarki ya shafi sana'ar gyaran janareto a Birnin kebbi | isyaku.com

Tun lokacin da aka sami canjin Gwamnati daga PDP zuwa APC a Najeriya,Gwamnatocin da suka shude sun yi iya nasu kokari domin sugan cewa sun wadatar da al'umma da wutan lantarki kamar Gwamnatocin soja har izuwa na farin hula lokacin mulkin Obasanjo zu 'Yar'adua amma basu cinma nassara ba.

A nan jihar Kebbi,musamman cikin garin Birnin kebbi da kewaye an sami wadatar wutan lantarki idan aka kwatanta da inda aka fito a sa'ilinda ake raba wuta kowane awa hudu.Ma'ana akan more wuta ne jimlar awa bakwai ko takwas a kowane awa 24.

A yanzu kuwa,akan more wutar lantarki a garin Birnin kebbi da kewaye akalla awa 12 zuwa 16 sai dan abin da ba'a rasa ba saboda matsaloli da kan shafi na'urorin wutar lantarkin.

Hakan ya haifar da koma baya ga masu sana'ar gyran na'urar bayarda wutar lantarki watau janareto.Ada can duk inda ka nufa idan dai mai gyaran janareto ne zaka ga cinkoso na jama'a a wajen gyaran,amma a yanzu cewa zakayi an share wajen sana'ar tasu ne idan bancin daidaikun janareto da akan kawo gyara wanda daga lokaci zuwa lokaci ne.

Bayanai sun nuna cewa akwai wadanda suka je aikin Hajji,sun gina gida kuma suka yi aure a sanadin sana'ar gyaran janareto,amma ala tilas suka canja sana'a saboda wadatar wutar lantarki a garin Birnin kebbi.

Duk da yake ana fuskantar matsalar yawan daukewan wutan lantarkin a yanzu haka a Birnin kebbi da kewaye,bincike ya nuna cewa hakan yana da nasaba ne da matsalar damana ida iska ke sanadin hadewar wayoyin lantarki sanadin da ke sa transfomomi ke bugawa sai ya haifar da daukewar wuta da sauran matsaloli.



Ku biyo mu a shafin mu na Facebook @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka sami labaranmu ta Whatsapp ? ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye kyauta a koda yaushe muka wallafa Labari. Kana da sha'awar taimaka mana da Labarai, ko sharhi ? ka kira mu a 08062543120. Shiga shafinmu kai tsaye domin samun cikakkun Labarai.Ka shiga www.isyaku.com a browser ko opera ko firefox ko safari na wayarka zaka sami cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN