• Labaran yau

  July 31, 2017

  Yadda aka daure yaro har kwana 3 a bisa zargin kasancewa Aljani

  Austin Segun uba ne ga yara uku a al'umman Eruemukohwarien  a karamar hukumar Ughelli ta gabas a jihar Delta wanda ya daure hannayen da kafafun dansa ya hada igiyar da karfen windo a gidansa har tsawon kwana uku bayan wani Pasto ya shaida masa cewa yaron Aljani ne.

  Bayanai sun nuna cewa 'yan banga ne suka ceci yaron a yayin da suka ji yana nufashi da kyar da misalin karfe 2:00 na dare kuma suka shaida wa DPO na sashe na "A"  wanda shi kuma ya kama mahaifin yaron.

  Rahotanni sun nuna cewa yaron ya shaida wa yansanda cewa ya sha fama da irin wannan gallazawa saboda mahaifiyarsa ta rasu kuma haka yake shan azaba a hannun kishiyar uwarsa.

  'Yansanda sun kai yaron babban Asibiti na Ughelli inda aka duba lafiyarsa.

  A bisa wannan dalili ne dattijan garin Ughelli suka yi zaman gaggawa inda suka kori Austin da matarsa daga garin Ughelli.


  Ku biyo mu a
  https://www.facebook.com/isyakuweb
  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120.
  Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120.
   Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Yadda aka daure yaro har kwana 3 a bisa zargin kasancewa Aljani Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama