• Labaran yau

  July 16, 2017

  Wasu jami'an tsaro sun harbe jami'an FRSC 2 a jihar Abia

  Hukumar kiyaye hadurra ta kasa FRSC ta tabbatar cewa wasu jami'an tsaro da ke tare da wani babban jami'in Gwamnatin jihar Abia sun harbi jami'anta su biyu wadanda ke bakin aika a jihar kamar yadda ganau ba jiyau ba ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN.

  Babban jami'i da ke fadakar da jama'a na rundunar a jihar ta Abia  Mr Bisi Kazeem ya tabbatar da aukuwar lamarin,amma bai fadi ko wane babban jami'in Gwamnatin jihar ne abin ya shafa ba.Amma ya yi bayani cewa 'yansanda suna bincike akan lamarin,yayinda hafsoshin hukumar da aka raunata suna jinya a wani Asibiti da ba'a bayyana inda yake ba.

  Bayanai sun nuna cewa lamarin ya faru ne bayan jami'an FRSC sun dakatar da motar da wasu mata ke ciki akan dalilin rashin amfani da bel na kiyaye lafiya (safety belt) sai matan suka fara zagin jami'an FRSC daga bisani wata mace ta kira dogarawan ta wadanda jamai'an tsaro ne daga zuwansu sai suka fara harbe harbe da bindiga wanda hakan ya haifar da raunuka ga wuyan daya daga cikin jami'an FRSC yayin da ragowar dayan ya sami rauni a kwankwaso da kafadarsa.
  Ku biyo mu a shafin mu na Facebook @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka sami labaranmu ta Whatsapp ? ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye kyauta a koda yaushe muka wallafa Labari. Kana da sha'awar taimaka mana da Labarai, ko sharhi ? ka kira mu a 08062543120. Shiga shafinmu kai tsaye domin samun cikakkun Labarai.Ka shiga www.isyaku.com a browser ko opera ko firefox ko safari na wayarka zaka sami cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Wasu jami'an tsaro sun harbe jami'an FRSC 2 a jihar Abia Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama