• Labaran yau

  July 24, 2017

  Sojin ruwan Najeriya ta kama sojojin ruwa na bogi

  Rudunar sojan ruwa na Najeriya ta damke wasu sojan ruwa na bogi wanda suka dade suna gabatar da ayyuka da sunan cewa su sojojin ruwa ne a jihar Rivers,sojojin da ke jirgin ruwan Najeriya mai suna  Shipyard Pathfinder sune suka kama sojin bogin.

  Kwamandan sashen liken asiri na rundunar na NNS Pathfinder, Commander Mamman Aluchi shi ya shaida wa manema labarai haka a garin Port Harcourt na jihar ta Rivers.

  A cewar Kwamandan "wadanan mutanen barazana ne ga lafiya da tsaron kasa"
  Ku biyo mu a
  https://www.facebook.com/isyakuweb
  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye.
  Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120.
  Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Sojin ruwan Najeriya ta kama sojojin ruwa na bogi Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama