Shugaba Buhari zai dowo Najeriya cikin mako 2 - Rochas

Bayanai da ke fitowa daga birnin London sun nuna cewa shugaba Muhammadu Buhari zai dawo Najeriya nan da sati biyu.

Gwamnan jihar Imo a tarayyar Najeriya Rochas Okorocha ya sahida wa BBC haka yayin da yake tattaunawa da su kasancewa yana daya daga cikin Gwamnoni hudu da suka kai wa shugaba Buhari ziyara a birnin London .

Gwamnan ya kara da cewa shugaban yana cikin koshin lafiya "kuma zancen da ake yi cewa yana cikin mawuyacin halin ba gaskiya ba ne. Yana nan lafiya lau."

"Na yi mamakin yadda na gan shi. Yana da koshin lafiya. Abubuwan da ake cewa game da rashin lafiyarsa ba haka muka gani ba," in ji gwamnan na jihar Imo.

Tawagar da ta ziyarci shugaban ta hada da gwamna Umar Tanko Almakura na jihar Nasarawa, da Nasir Elrufai na jihar Kaduna da kuma Yahaya Bello na jihar Kogi. Sai kuma Shugaban Jam'iyyar na kasa Cif John Oyegun da Ministan Sufuri Rotimi Ameachi.

A cewar Mista Okorocha sun dauki kimanin sa'a guda suna cin liyafa tare da shugaban kasar a bayyanarsa ta farko a bainar jama'a tun bayan da ya tafi jinya a birnin London kwanaki 78 da suka gabata.
Ku biyo mu a
https://www.facebook.com/isyakuweb
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye.
Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120.
Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.
Shugaba Buhari zai dowo Najeriya cikin mako 2 - Rochas Shugaba Buhari zai dowo Najeriya cikin mako 2 - Rochas Reviewed by on July 24, 2017 Rating: 5

No comments:

Rubuta ra ayin ka

ISYAKU TV

Powered by Blogger.