Shakku kan kasancewar shinkafar roba a kasuwannin Najeriya | isyaku.com

Akwai labari da ya dade yana zagayawa ta kafar sada zumunta na yanar gizo wanda ke nuna cewa akwai shinkafar roba da ake zargin kasar China ta shigo da shi wasu kasashen Africa da suka hada da Senegal,Ghana,Gambia da Najeriya.

Duk da rashin tabbatar da ingancin wannan zargin a bayyane,kamar yadda hukumomi suka tabbatar a Najeriya cewa jita-jita ne kawai ake bazawa akan lamarin shinkafar roba a cikin kasar.

Hakazalika hukumomi a kasashen Gambia,Ghana da Senegal sun kaddamar da bincike akan zargin cewa ana shiga kasashen da shinkafar roba,amma daga karshe babu sahihancin gaskiya a kan lamarin.

Duk da wannan bincike daga hukumomi a kasashen da ake zargin bayyanar shinkafar roba a cikin su,bisa ga dukkanin alamu har yanzu wasu mutane sun gaskata cewa akwai shinkafar ta roba ko da yake wasu cikin masu gaskata wannan lamarin basu taba ganin wannan shinkafar ba saidai yadda aka yi bayani a shafukan sada zumunta da kuma wasu hotuna da ake sanyawa wanda ke nuna cewa shinkaface ta roba.




Ku biyo mu a shafin mu na Facebook @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka sami labaranmu ta Whatsapp ? ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye kyauta a koda yaushe muka wallafa Labari. Kana da sha'awar taimaka mana da Labarai, ko sharhi ? ka kira mu a 08062543120. Shiga shafinmu kai tsaye domin samun cikakkun Labarai.Ka shiga www.isyaku.com a browser ko opera ko firefox ko safari na wayarka zaka sami cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN